Skip to content

Cilicia

8 verses

36.9100, 34.8900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Cilicia

  1. Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,

  2. Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.

  3. Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

  4. Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”

  5. “Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.

  6. Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne,

  7. Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya.

  8. Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya.