- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 95
The Revelation
John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ru’uya ta Yohanna 1:1kusan 96 M.
Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,
- Ru’uya ta Yohanna 1:2kusan 96 M.
wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi.
- Ru’uya ta Yohanna 1:3kusan 96 M.
Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.
- Ru’uya ta Yohanna 1:4kusan 96 M.
Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa,
- Ru’uya ta Yohanna 1:5kusan 96 M.
da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa,
- Ru’uya ta Yohanna 1:6kusan 96 M.
ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.
- Ru’uya ta Yohanna 1:7kusan 96 M.
“Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”
- Ru’uya ta Yohanna 1:8kusan 96 M.
“Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”
- Ru’uya ta Yohanna 1:9kusan 96 M.
Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu.
- Ru’uya ta Yohanna 1:10kusan 96 M.
A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho,
- Ru’uya ta Yohanna 1:11kusan 96 M.
wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”
- Ru’uya ta Yohanna 1:12kusan 96 M.
Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya.
- Ru’uya ta Yohanna 1:13kusan 96 M.
A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa.
- Ru’uya ta Yohanna 1:14kusan 96 M.
Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta.
- Ru’uya ta Yohanna 1:15kusan 96 M.
Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu.
- Ru’uya ta Yohanna 1:16kusan 96 M.
A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
- Ru’uya ta Yohanna 1:17kusan 96 M.
Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe.
- Ru’uya ta Yohanna 1:18kusan 96 M.
Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.
- Ru’uya ta Yohanna 1:19kusan 96 M.
“Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba.
- Ru’uya ta Yohanna 1:20kusan 96 M.
Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.
- Ru’uya ta Yohanna 2:1kusan 96 M.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
- Ru’uya ta Yohanna 2:2kusan 96 M.
Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.
- Ru’uya ta Yohanna 2:3kusan 96 M.
Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
- Ru’uya ta Yohanna 2:4kusan 96 M.
Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko.
- Ru’uya ta Yohanna 2:5kusan 96 M.
Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake.