- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 95
The Revelation
John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ru’uya ta Yohanna 2:6kusan 96 M.
Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.
- Ru’uya ta Yohanna 2:7kusan 96 M.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
- Ru’uya ta Yohanna 2:8kusan 96 M.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.
- Ru’uya ta Yohanna 2:9kusan 96 M.
Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.
- Ru’uya ta Yohanna 2:10kusan 96 M.
Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
- Ru’uya ta Yohanna 2:11kusan 96 M.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.
- Ru’uya ta Yohanna 2:12kusan 96 M.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu.
- Ru’uya ta Yohanna 2:13kusan 96 M.
Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.
- Ru’uya ta Yohanna 2:14kusan 96 M.
Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.
- Ru’uya ta Yohanna 2:15kusan 96 M.
Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa.
- Ru’uya ta Yohanna 2:16kusan 96 M.
Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.
- Ru’uya ta Yohanna 2:17kusan 96 M.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.
- Ru’uya ta Yohanna 2:18kusan 96 M.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge.
- Ru’uya ta Yohanna 2:19kusan 96 M.
Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.
- Ru’uya ta Yohanna 2:20kusan 96 M.
Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.
- Ru’uya ta Yohanna 2:21kusan 96 M.
Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya.
- Ru’uya ta Yohanna 2:22kusan 96 M.
Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta.
- Ru’uya ta Yohanna 2:23kusan 96 M.
Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.
- Ru’uya ta Yohanna 2:24kusan 96 M.
Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba.
- Ru’uya ta Yohanna 2:25kusan 96 M.
Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’
- Ru’uya ta Yohanna 2:26kusan 96 M.
Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai.
- Ru’uya ta Yohanna 2:27kusan 96 M.
‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’kamar yadda na karɓi iko daga Ubana.
- Ru’uya ta Yohanna 2:28kusan 96 M.
Zan kuma ba shi tauraron asubahi.
- Ru’uya ta Yohanna 2:29kusan 96 M.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.
- Ru’uya ta Yohanna 3:1kusan 96 M.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne.