Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus

607 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutumin ya ce, “Babu ko ɗaya, na dai zo ne a matsayin shugaban rundunar sojojin Ubangiji.” Sai Yoshuwa ya kwanta da fuskarsa har ƙasa, ya girmama shi, ya ce masa, “Ranka yă daɗe, wane saƙo kake da shi domin bawanka?”

  2. Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa.

  3. Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,

  4. yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’

  5. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?

  6. Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.

  7. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”

  8. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.

  9. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”

  10. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.

  11. Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.

  12. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.

  13. Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela

  14. Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.

  15. Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;

  16. ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.

  17. Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’

  18. Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.”

  19. Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,

  20. zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;

  21. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.

  22. Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.

  23. “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai,

  24. don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

  25. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure wadda na kora? Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne na sayar da kai? Saboda zunubanka aka sayar da kai; saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.