Skip to content

Tyre

52 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Tyrus

33.2700, 35.1900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Tyre

Tace bisa littafi
  1. Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,

  2. To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.

  3. Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda.

  4. Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa.

  5. Sarki Solomon ya aika zuwa Taya aka kuma kawo Huram,

  6. wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi.

  7. sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki.

  8. Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba.

  9. To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada.

  10. Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki.

  11. Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”

  12. wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.

  13. Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.

  14. Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya.

  15. “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”

  16. Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.

  17. Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.

  18. Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?

  19. A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,

  20. A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.

  21. dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;

  22. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  23. Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor.

  24. “Ɗan mutum, domin Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Yauwa! Ƙofar zuwa al’ummai ta karye, an kuma buɗe mini ƙofofinta; yanzu da take kufai zan wadace,’

  25. saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da ke, ya Taya, zan kuwa kawo al’ummai masu yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.