Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sea

95 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

  2. Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.”

  3. Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

  4. Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.”

  5. Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).

  6. tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,

  7. “Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.

  8. Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar.

  9. Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.

  10. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  11. Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne.

  12. “Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku.

  13. “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.

  14. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”

  15. Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

  16. Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.

  17. Za su kira mutane zuwa dutse, a can za su miƙa hadayun adalci; za su yi biki a yalwan tekuna, a dukiyoyin da aka ɓoye a cikin yashi.”

  18. da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,

  19. Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku.

  20. Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.

  21. Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.

  22. Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.

  23. ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

  24. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

  25. Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,