Skip to content

Cyrus

19 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Cyrus

  1. Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,

  2. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”

  3. A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,

  4. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.

  5. Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.

  6. Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.

  7. Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.

  8. Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.”

  9. Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa.

  10. “Duk da haka, a shekara ta farko ta mulkin Sairus sarkin Babilon, Sarki Sairus ya ba da umarni cewa a sāke gina wannan gidan Allah.

  11. Ya kuma kwashe kwanonin zinariya da azurfa na gidan Allah daga haikalin Babilon waɗanda Nebukadnezzar ya kwasa daga haikali a Urushalima. Sa’an nan sarki Sairus ya ba wa wani mutum mai suna Sheshbazzar umarni wanda ya sa ya zama gwamna,

  12. Yanzu in sarki yana so, bari a duba cikin littattafan tarihi na sarakuna na Babilon a gani ko lalle sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina gidan Allah a Urushalima. Bari sarki yă aiko mana da abin da ya gani game da wannan abu.

  13. A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce, Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in.

  14. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.

  15. wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’

  16. “Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.

  17. Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus.

  18. Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa.

  19. A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.