Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Medo-Persian Kingdom

62 ayoyi · 34 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

  2. Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.

  3. Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,

  4. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”

  5. A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,

  6. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.

  7. Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima.

  8. Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ”

  9. A farkon mulkin Zerzes, sai abokan gāba suka kawo ƙarar mutanen Yahuda da na Urushalima.

  10. A zamanin Artazerzes sarkin Farisa kuma, sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da sauran abokansu suka rubuta wasiƙa zuwa ga Artazerzes. Aka rubuta wasiƙar da harufan Arameyik, aka kuma fassara ta a yaren Arameyik.

  11. Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.

  12. Sai aka sami takarda a Ekbatana a yankin Mediya, ga kuma abin da yake rubuce a ciki. Abin tunawa.

  13. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.

  14. Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila.

  15. Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya,

  16. Artazerzes, sarkin sarakuna. Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama. Gaisuwa.

  17. Amma yayinda dukan wannan yake faruwa, ba ni a Urushalima, gama a shekara ta talatin da biyu na Artazerzes sarkin Babilon na dawo wurin sarki. A wani lokaci daga baya na nemi izininsa

  18. Ga abin da ya faru a zamanin Zerzes. Zerzes ya yi mulki bisan larduna 127 daga Indiya zuwa Kush.

  19. A lokacin nan, Sarki Zerzes ya yi mulki daga gadon sarauta, cikin mazaunin masarautar Shusha.

  20. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya yi wa dukan hakimansa da ma’aikatansa liyafa. Shugabannin mayaƙan Farisa, da Mediya, da yerimai; da kuma hakimai na lardunan suka kasance.

  21. Kwanaki 180 cif, ya nuna yawan dukiyar masarautarsa, da ɗaukakarta da kuma darajar girmansa.

  22. Sa’ad da waɗannan kwanaki suka wuce, sai sarki ya yi liyafa a cikin lambun da aka shinge na fadar sarki wadda ta ɗauki kwana bakwai wa dukan mutane daga ƙarami har zuwa babba, waɗanda suke zama a masarautar Shusha.

  23. Aka rarraba ruwan inabi cikin kwaf na zinariya, kowanne kuwa dabam yake da ɗayan. Ruwan inabin kuwa yana da yawa, bisa ga wadatar sarki.

  24. Bisa ga umarnin sarki, aka bar kowane baƙo yă sha yadda ya ga dama, gama sarki ya umarci dukan bayin da suke rarraba ruwan inabin su ba wa kowa abin da yake so.

  25. Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta