- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Creation Era
The Tower of Babel
Scattered nations and confused languages mark the beginning of the diversity of peoples across the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
- Farawa 10:4kusan 2338 K.H.
’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
- Farawa 10:5kusan 2247 K.H.
(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
- Farawa 10:6kusan 2228 K.H.
’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
- Farawa 10:7kusan 2228 K.H.
’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
- Farawa 10:8kusan 2289 K.H.
Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
- Farawa 10:9kusan 2289 K.H.
Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
- Farawa 10:10kusan 2259 K.H.
Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
- Farawa 10:11kusan 2304 K.H.
Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
- Farawa 10:12kusan 2304 K.H.
da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
- Farawa 10:13kusan 2304 K.H.
Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
- Farawa 10:14kusan 2304 K.H.
Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
- Farawa 10:15kusan 2304 K.H.
Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
- Farawa 10:16kusan 2304 K.H.
Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
- Farawa 10:17kusan 2304 K.H.
Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
- Farawa 10:18kusan 2304 K.H.
Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
- Farawa 10:19kusan 2304 K.H.
har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
- Farawa 10:20kusan 2304 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
- Farawa 10:21kusan 2304 K.H.
Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
- Farawa 10:22kusan 2304 K.H.
’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
- Farawa 10:23kusan 2304 K.H.
’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
- Farawa 10:24kusan 2304 K.H.
Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
- Farawa 10:25kusan 2247 K.H.
Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.