Tsallake zuwa abun ciki

Creation Era

The Tower of Babel

Scattered nations and confused languages mark the beginning of the diversity of peoples across the earth.

64 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 11:19kusan 2008 K.H.

    Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  2. Farawa 11:20kusan 2185 K.H.

    Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.

  3. Farawa 11:21kusan 1978 K.H.

    Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  4. Farawa 11:22kusan 2155 K.H.

    Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.

  5. Farawa 11:23kusan 1955 K.H.

    Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  6. Farawa 11:24kusan 2126 K.H.

    Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.

  7. Farawa 11:25kusan 2007 K.H.

    Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  8. Farawa 11:26kusan 2056 K.H.

    Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.

  9. Farawa 11:27kusan 1996 K.H.

    Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.

  10. Farawa 11:28kusan 1996 K.H.

    Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.

  11. Farawa 11:29kusan 1996 K.H.

    Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.

  12. Farawa 11:30kusan 1996 K.H.

    Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.

  13. Farawa 11:31kusan 1926 K.H.

    Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.

  14. Farawa 11:32kusan 1921 K.H.

    Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.