Skip to content

Gaza

19 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Azzah

31.5200, 34.4300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Gaza

  1. har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.

  2. Yoshuwa ya ci su da yaƙi daga Kadesh Barneya zuwa Gaza, da kuma daga dukan yankin Goshen zuwa Gibeyon.

  3. Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai.

  4. Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.

  5. Mutanen Yahuda kuma suka ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa.

  6. Sukan yi sansani a ƙasar sun lalatar da hatsi har zuwa Gaza kuma ba sa barin wani abu mai rai wa Isra’ila, ko tumaki ko shanu ko jakuna.

  7. Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana.

  8. Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku.

  9. Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

  10. Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe.

  11. Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.

  12. da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);

  13. Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.

  14. Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku?

  15. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom,

  16. Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta.

  17. Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron.

  18. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.

  19. To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”