Tsallake zuwa abun ciki

Joshua

189 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Oshea, Jehoshua, Hoshea, Jeshua, Jesus

Ayoyin da suka ambaci Joshua

Tace bisa littafi
  1. Musa ya ce wa Yoshuwa, “Zaɓi waɗansu mazanmu, ka je ka yaƙi Amalekawa. Gobe zan tsaya a bisa tudu, da sandan Allah a hannuwana.”

  2. Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu.

  3. Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi.

  4. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta wannan a cikin littafi, yă zama abin tuni, ka kuma faɗa wa Yoshuwa zan hallaka Amalekawa ƙaƙaf daga duniya.”

  5. Sa’an nan Musa ya fita tare da Yoshuwa mataimakinsa, ya kuwa hau kan dutsen Allah.

  6. Sa’ad da Yoshuwa ya ji surutun mutane suna ihu, sai ya ce wa Musa, “Kamar akwai ƙarar yaƙi a sansani.”

  7. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.

  8. Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”

  9. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

  10. Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)

  11. Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu

  12. Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  13. Daga cikin mutanen da suka leƙo asirin ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun, da Kaleb ɗan Yefunne ne, kaɗai suka rayu.

  14. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutumin da ruhun shugabanci yake a cikinsa, ka ɗibiya masa hannunka.

  16. Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Yoshuwa, ya sa ya tsaya a gaban Eleyazar firist, da kuma gaban dukan jama’a.

  17. ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’

  18. Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,

  19. “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.

  20. Amma mataimakinka, Yoshuwa ɗan Nun, zai shiga. Ka ƙarfafa shi gama shi ne zai jagoranci Isra’ila su gāje ta.

  21. A lokacin nan na umarci Yoshuwa na ce, “Da idanunka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan sarakuna biyu. Haka Ubangiji zai yi da dukan masarautai a can, inda za ku.

  22. Amma ka umarci Yoshuwa, ka ƙarfafa shi, ka kuma ba shi ƙarfin gwiwa, gama shi ne zai jagoranci wannan mutane su haye, yă kuma ba su gādon ƙasar da za ka gani.”

  23. Ubangiji Allahnku kansa zai haye a gabanku. Zai hallaka waɗannan al’ummai da suke gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu. Yoshuwa shi ma zai haye a gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.

  24. Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu.

  25. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.