Skip to content

Nun

30 ayoyi · 2 'yan gida

An kuma san shi da: Non

Ayoyin da suka ambaci Nun

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.

  2. Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”

  3. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

  4. Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)

  5. Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu

  6. Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  7. Daga cikin mutanen da suka leƙo asirin ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun, da Kaleb ɗan Yefunne ne, kaɗai suka rayu.

  8. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  9. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutumin da ruhun shugabanci yake a cikinsa, ka ɗibiya masa hannunka.

  10. ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’

  11. Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,

  12. “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.

  13. Amma mataimakinka, Yoshuwa ɗan Nun, zai shiga. Ka ƙarfafa shi gama shi ne zai jagoranci Isra’ila su gāje ta.

  14. Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.”

  15. Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane.

  16. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  17. Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,

  18. Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can.

  19. Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.

  20. Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, “Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa.”

  21. Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu.

  22. Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.

  23. Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu,

  24. Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.

  25. To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a