Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Land

108 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,

  2. kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.

  3. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

  4. “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.

  5. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.

  6. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.

  7. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.

  8. Ubangiji ya ce wa Musa,

  9. “Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”

  10. Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.

  11. Shugabannin kuwa su ne, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;

  12. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;

  13. Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

  14. Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;

  15. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

  16. daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;

  17. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;

  18. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);

  19. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;

  20. Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;

  21. Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;

  22. Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.

  23. Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)

  24. Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.

  25. Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.