Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Land: As at first divided

12 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da As at first divided

  1. Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.

  3. “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,

  4. tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,

  5. inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.

  6. “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.

  7. “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,

  8. za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,

  9. tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.

  10. “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.

  11. Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.

  12. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”