Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Land: Divided by lot

22 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da Divided by lot

  1. Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.

  3. Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.

  4. “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

  5. Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon

  6. Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;

  7. Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;

  8. Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;

  9. Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;

  10. Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;

  11. Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;

  12. Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;

  13. Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”

  14. Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.

  15. ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”

  16. Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.

  17. Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,

  18. da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.

  19. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,

  20. wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.

  21. Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.

  22. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.