Skip to content

Benjamin

157 ayoyi · 26 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Benjamin

Tace bisa littafi
  1. Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.

  2. ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin.

  3. Amma Yaƙub bai aiki Benyamin, ɗan’uwan Yusuf tare da sauran ba, gama yana tsoro kada wani abu yă faru da shi.

  4. Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!”

  5. Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”

  6. Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf.

  7. Sa’ad da Yusuf ya ga Benyamin tare da su, sai ya ce wa mai hidimar gidansa, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”

  8. Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.”

  9. Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

  10. Sa’an nan mai hidimar ya fara bincike, farawa daga babba, ya ƙare a ƙaramin. Aka kuwa sami kwaf ɗin a buhun Benyamin.

  11. “Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku.

  12. Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka.

  13. Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar.

  14. ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.

  15. ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.

  16. “Benyamin kyarkeci ne mai kisa; da safe yakan cinye abin da ya farauto da yamma yakan raba ganima.”

  17. Issakar, Zebulun da Benyamin;

  18. daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;

  19. Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  20. Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.

  21. Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.

  22. A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.

  23. Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.

  24. daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;

  25. Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu, daga Bela, kabilar Belawa; daga Ashbel, kabilar Ashbelawa; daga Ahiram, kabilar Ahiramawa;