Skip to content

Gad

55 ayoyi · 21 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Gad

Tace bisa littafi
  1. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.

  2. ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.

  3. ’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.

  4. “Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su.

  5. Dan da Naftali; Gad da Asher.

  6. daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;

  7. Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  8. Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.

  9. Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel.

  10. A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.

  11. Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad.

  12. Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.

  13. Zuriyar Gad bisa ga kabilansu, daga Zafon, kabilar Zafonawa; daga Haggi, kabilar Haggiwa; daga Shuni, kabilar Shunawa;

  14. Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500.

  15. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.

  16. Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,

  17. Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?

  18. Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta.

  19. ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu.

  20. Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa.

  21. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.

  22. Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower,

  23. saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.

  24. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

  25. Game da Gad ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fadada mazaunin Gad! Gad yana zama a can kamar zaki, yana yayyage a hannu da kai.