Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza, waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub; kowanne da iyalinsa.

  2. Ruben, Simeyon, Lawi da Yahuda;

  3. Issakar, Zebulun da Benyamin;

  4. Dan da Naftali; Gad da Asher.

  5. Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar.

  6. Fitowa 1:6kusan 1635 K.H.

    Yanzu Yusuf da dukan ’yan’uwansa da kuma dukan tsaran nan da suka tafi Masar, sun mutu,

  7. Fitowa 1:7kusan 1635 K.H.

    amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su.

  8. Fitowa 1:8kusan 1635 K.H.

    Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar.

  9. Fitowa 1:9kusan 1635 K.H.

    Ya ce wa mutanensa, “Duba Isra’ilawa sun yi yawa, sun fi ƙarfinmu.

  10. Fitowa 1:10kusan 1635 K.H.

    Ku zo, mu yi dabara a kansu, in ba haka ba za su ƙaru fiye da haka, in kuwa yaƙi ya tashi tsakaninmu da abokan gāba, za su iya haɗa kai da abokan gāba, su yaƙe mu, su bar ƙasar.”

  11. Fitowa 1:11kusan 1635 K.H.

    Saboda haka sai suka naɗa shugabannin gandu a kansu don su wahalshe su, su kuma bauta musu, suka sa su suka gina biranen Fitom da Rameses su zama biranen ajiya, domin Fir’auna.

  12. Fitowa 1:12kusan 1635 K.H.

    Amma duk da wannan ƙarin wulaƙancin da ake yi musu, su kuwa sai daɗa riɓaɓɓanya suke ta yi. Sai tsoron Isra’ilawa ya ƙaru a zuciyar Masarawa,

  13. Fitowa 1:13kusan 1635 K.H.

    ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala.

  14. Fitowa 1:14kusan 1635 K.H.

    Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan.

  15. Fitowa 1:15kusan 1635 K.H.

    Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce,

  16. Fitowa 1:16kusan 1635 K.H.

    “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.”

  17. Fitowa 1:17kusan 1635 K.H.

    Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu.

  18. Fitowa 1:18kusan 1635 K.H.

    Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?”

  19. Fitowa 1:19kusan 1635 K.H.

    Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”

  20. Fitowa 1:20kusan 1635 K.H.

    Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā.

  21. Fitowa 1:21kusan 1635 K.H.

    Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.

  22. Fitowa 1:22kusan 1573 K.H.

    Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.”

  23. Fitowa 2:1kusan 1572 K.H.

    Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya,

  24. Fitowa 2:2kusan 1571 K.H.

    ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku.

  25. Fitowa 2:3kusan 1571 K.H.

    Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin.