Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Fitowa 15:13kusan 1491 K.H.

    A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe mutanen da ka fansa. A cikin ƙarfinka, za ka bishe su zuwa mazauninka mai tsarki.

  2. Fitowa 15:14kusan 1491 K.H.

    Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya.

  3. Fitowa 15:15kusan 1491 K.H.

    Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.

  4. Fitowa 15:16kusan 1491 K.H.

    Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.

  5. Fitowa 15:17kusan 1491 K.H.

    Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka, wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.

  6. Fitowa 15:18kusan 1491 K.H.

    “Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”

  7. Fitowa 15:19kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

  8. Fitowa 15:20kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.

  9. Fitowa 15:21kusan 1491 K.H.

    Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.”

  10. Fitowa 15:22kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.

  11. Fitowa 15:23kusan 1491 K.H.

    Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).

  12. Fitowa 15:24kusan 1491 K.H.

    Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”

  13. Fitowa 15:25kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su.

  14. Fitowa 15:26kusan 1491 K.H.

    Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”

  15. Fitowa 15:27kusan 1491 K.H.

    Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.