Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Fitowa 13:16kusan 1491 K.H.

    Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.”

  2. Fitowa 13:17kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.”

  3. Fitowa 13:18kusan 1491 K.H.

    Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.

  4. Fitowa 13:19kusan 1491 K.H.

    Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”

  5. Fitowa 13:20kusan 1491 K.H.

    Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada.

  6. Fitowa 13:21kusan 1491 K.H.

    Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana.

  7. Fitowa 13:22kusan 1491 K.H.

    Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.

  8. Fitowa 14:1kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  9. Fitowa 14:2kusan 1491 K.H.

    “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  10. Fitowa 14:3kusan 1491 K.H.

    Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’

  11. Fitowa 14:4kusan 1491 K.H.

    Zan kuma taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi su. Na shirya wannan domin in nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da ƙungiyar sojansa. Bayan wannan, mutanen Masar za su sani ni ne Ubangiji.” Sai Isra’ilawa suka yi haka.

  12. Fitowa 14:5kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da aka faɗa wa Fir’auna cewa Isra’ilawa sun gudu, sai Fir’auna da bayinsa suka canja ra’ayinsu game da su, suka ce, “Me muka yi? Mun bar Isra’ilawa suka tafi, mun kuwa rasa hidimarsu!”

  13. Fitowa 14:6kusan 1491 K.H.

    Sai shi da keken yaƙinsa suka shirya, ya kuma ɗauki sojojinsa tare da shi.

  14. Fitowa 14:7kusan 1491 K.H.

    Ya ɗauki kekunan yaƙi ɗari shida mafi kyau duka, tare da duk sauran keken yaƙin Masar, da shugabanni kuma a kan dukansu.

  15. Fitowa 14:8kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna sarkin Masar, domin yă bi Isra’ilawa waɗanda suke tafiya ba tsoro.

  16. Fitowa 14:9kusan 1491 K.H.

    Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  17. Fitowa 14:10kusan 1491 K.H.

    Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji.

  18. Fitowa 14:11kusan 1491 K.H.

    Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar?

  19. Fitowa 14:12kusan 1491 K.H.

    Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!”

  20. Fitowa 14:13kusan 1491 K.H.

    Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba.

  21. Fitowa 14:14kusan 1491 K.H.

    Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”

  22. Fitowa 14:15kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Don me kake mini kuka? Ka faɗa wa Isra’ilawa su ci gaba da tafiya.

  23. Fitowa 14:16kusan 1491 K.H.

    Ka ɗaga sandanka, ka miƙa shi bisa teku don ruwa yă rabu domin Isra’ilawa su wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa.

  24. Fitowa 14:17kusan 1491 K.H.

    Zan taurare zukatan Masarawa su shiga don su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.

  25. Fitowa 14:18kusan 1491 K.H.

    Masarawa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.”