Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Fitowa 12:42kusan 1491 K.H.

    Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.

  2. Fitowa 12:43kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Waɗannan ne ƙa’idodin Bikin Ƙetarewa. “Ba baƙon da zai ci shi.

  3. Fitowa 12:44kusan 1491 K.H.

    Duk bawan da kuka sayo, yana iya ci, in dai an yi masa kaciya,

  4. Fitowa 12:45kusan 1491 K.H.

    amma wanda ba ya zama tare da ku na ɗinɗinɗin, da kuma wanda aka ɗauki hayansa, ba zai ci ba.

  5. Fitowa 12:46kusan 1491 K.H.

    “Dole a ci shi a cikin gida ɗaya; kada a kai naman waje. Kada a karya wani daga ƙasusuwansa.

  6. Fitowa 12:47kusan 1491 K.H.

    Dole dukan taron jama’ar Isra’ila su yi bikin.

  7. Fitowa 12:48kusan 1491 K.H.

    “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa.

  8. Fitowa 12:49kusan 1491 K.H.

    Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”

  9. Fitowa 12:50kusan 1491 K.H.

    Dukan Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

  10. Fitowa 12:51kusan 1491 K.H.

    A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.

  11. Fitowa 13:1kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  12. Fitowa 13:2kusan 1491 K.H.

    “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

  13. Fitowa 13:3kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya ce wa mutane, “Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga ƙasar bauta, gama Ubangiji ya fito da ku da hannu mai iko. Kada ku ci wani abin da yake da yisti.

  14. Fitowa 13:4kusan 1491 K.H.

    A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib.

  15. Fitowa 13:5kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.

  16. Fitowa 13:6kusan 1491 K.H.

    Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, a kan rana ta bakwai kuma za ku yi biki ga Ubangiji.

  17. Fitowa 13:7kusan 1491 K.H.

    Ku ci burodi marar yisti cikin kwana bakwai; kada a sami wani abu mai yisti a cikinku, ko a sami yisti a ko’ina a wurinku.

  18. Fitowa 13:8kusan 1491 K.H.

    A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’

  19. Fitowa 13:9kusan 1491 K.H.

    Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko.

  20. Fitowa 13:10kusan 1491 K.H.

    Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta.

  21. Fitowa 13:11kusan 1491 K.H.

    “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku,

  22. Fitowa 13:12kusan 1491 K.H.

    sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne.

  23. Fitowa 13:13kusan 1491 K.H.

    Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin ’ya’yanku.

  24. Fitowa 13:14kusan 1491 K.H.

    “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta.

  25. Fitowa 13:15kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’