Skip to content

Bashan

52 verses

32.8000, 35.9300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Bashan

Tace bisa littafi
  1. Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi.

  2. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.

  3. Wannan ya faru bayan ya ci Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi mulki a Heshbon da yaƙi. A Edireyi kuma ya ci Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot da yaƙi.

  4. Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi.

  5. Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba.

  6. A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan.

  7. Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan.

  8. (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)

  9. Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa.

  10. Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.

  11. Suka mallaki ƙasarsa da kuma ƙasar Og sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa, gabas da Urdun.

  12. Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi.

  13. da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.

  14. Game da Dan ya ce, “Dan ɗan zaki ne, yana tsalle daga Bashan.”

  15. da kuma duk abubuwan da ya yi wa sarakuna biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot.

  16. Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.

  17. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

  18. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,

  19. wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.

  20. Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,

  21. da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.

  22. Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai.

  23. Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun,

  24. A hayin Urdun, gabas da Yeriko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ruben, Ramot cikin Gileyad a kabilar Gad, da Golan cikin Bashan a kabilar Manasse.

  25. Aka kuma ba wa zuriyar Gershon garuruwa goma sha uku daga iyalan kabilan Issakar, Asher, Naftali, da kuma rabin kabilar Manasse a Bashan.