Skip to content

Bashan

52 verses

32.8000, 35.9300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Bashan

Tace bisa littafi
  1. Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan;

  2. (Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare ’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka,

  3. Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);

  4. Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.

  5. gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.

  6. Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.

  7. Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.

  8. Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.

  9. Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).

  10. Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.

  11. Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;

  12. “Ka ba su mulkoki da al’ummai, kana ba su har ma da ƙasashen da suke jeji. Suka ci ƙasar Sihon na sarkin Heshbon da ƙasar Og inda sarkin Bashan yake mulki.

  13. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

  14. Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.

  15. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,

  16. Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana,

  17. Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  18. domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,

  19. Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.

  20. “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.

  21. Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad.

  22. Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.

  23. Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan.

  24. Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”

  25. Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā.