Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Manasseh

56 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Yusuf kuringa ce mai ba da amfani. Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi wadda rassanta na hawan bango.

  2. Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa; suka harbe shi babu tausayi.

  3. Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,

  4. saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa.

  5. Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.

  6. A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.

  7. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  8. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  9. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  10. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  11. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.

  12. Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.

  13. Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;

  14. daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem;

  15. daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa.

  16. (Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)

  17. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.

  18. Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce,

  19. “Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba.

  20. Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”

  21. Saboda haka Musa ya kawo maganarsu a gaban Ubangiji.

  22. Ubangiji kuwa ya ce wa masa,

  23. “Abin da ’ya’yan nan mata na Zelofehad suke faɗi gaskiya ne. Dole ka ba su mallaka a matsayin gādo cikin ’yan’uwan mahaifinsu, ka kuma mayar musu da gādon mahaifinsu.

  24. Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.

  25. Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.