Skip to content

Gilead

11 ayoyi · 11 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Gilead

  1. Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.

  2. Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;

  3. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.

  4. Sai shugabannin gidajen iyalan Gileyad ɗan Makir, ɗan Manasse, waɗanda suka fito daga kabilar zuriyar Yusuf, suka zo, suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, shugabannin iyalan Isra’ilawa.

  5. Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai.

  6. Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.

  7. Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”

  8. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.

  9. (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.

  10. Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.

  11. Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.