Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gilead
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.
Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;
Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce.
Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”