Skip to content

Gilead

80 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Gileadites

32.0400, 35.7200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Gilead

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya gudu da dukan abin da ya mallaka, ya ƙetare Kogi, ya nufi yankin tuddan Gileyad.

  2. Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad.

  3. Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma.

  4. Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.

  5. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.

  6. ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad.

  7. ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu.

  8. Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.

  9. Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.

  10. Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu.

  11. Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan.

  12. Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.

  13. Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa.

  14. Na kuma ba da Gileyad ga Makir.

  15. Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa.

  16. Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.

  17. Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,

  18. Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.

  19. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

  20. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,

  21. Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,

  22. da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.

  23. Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai.

  24. Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun,

  25. domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad.