Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Bashan

13 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan.

  2. (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)

  3. Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.

  4. Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa.

  5. Yayir na zuriyar Manasse ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawwot Yayir.)

  6. Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.

  7. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

  8. Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

  9. Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.

  10. Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,

  11. da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.

  12. A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu

  13. gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.