Skip to content

Ephraim

160 ayoyi · 9 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ephraim

Tace bisa littafi
  1. Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”

  2. A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.

  3. Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi.

  4. “To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa.

  5. Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.

  6. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.

  7. Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.

  8. Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.

  9. Ya kuma ga tsara ta uku ta ’ya’yan Efraim. Haka ma ’ya’yan Makir ɗan Manasse, an haife su aka sa a gwiwoyin Yusuf.

  10. daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;

  11. Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  12. Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne.

  13. Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.

  14. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.

  15. A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.

  16. Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba.

  17. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

  18. Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.

  19. Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu, daga Shutela, kabilar Shutelawa; daga Beker, kabilar Bekerawa; daga Tahan, kabilar Tahanawa.

  20. Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu.

  21. Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;

  22. Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”

  23. da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,

  24. gama ’ya’yan Yusuf sun zama kabilu biyu, Manasse da Efraim. Ba a ba Lawiyawa gādon ba sai dai garuruwan da aka ba su su zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau domin dabbobinsu.

  25. Wannan ne yankin da aka ba wa Manasse da Efraim zuriyar Yusuf gādonsu.