Tsallake zuwa abun ciki

Ephraim

160 ayoyi · 9 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ephraim

Tace bisa littafi
  1. Yankin Efraim ke nan bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kama daga Atarot Addar a gabas zuwa Bet-Horon,

  2. Daga Taffuwa kuma iyakar ta bi yamma zuwa kwazazzaban Kana, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne gādon mutanen Efraim bisa ga iyalansu.

  3. Gādon ya kuma haɗa da dukan garuruwa da ƙauyuka waɗanda aka keɓe wa mutanen Efraim daga cikin gādon mutanen Manasse.

  4. (Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.)

  5. Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum.

  6. Ƙasar a wajen kudu ta Efraim ce, ta wajen arewa kuma ta Manasse ce. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Asher yana wajen arewa, Issakar kuma a wajen gabas.

  7. Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Yusuf, wa Efraim da Manasse, “Kuna da yawa, kuna kuma da ƙarfi sosai. Ba wuri ɗaya kaɗai za ku samu gādo ba,

  8. Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.

  9. Sauran Kohatawan kuma aka ba su garuruwa goma daga iyalan kabilar Efraim, Dan da kuma rabi kabilar Manasse.

  10. Aka kuma ba wa sauran Kohatawa, iyalan Lawiyawa, garuruwa daga kabilar Efraim.

  11. A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer,

  12. Suka kuma binne shi a ƙasarsa ta gādo, a Timnat Sera a ƙasar kan tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.

  13. Eleyazar ɗan Haruna, ya mutu aka binne shi a Gibeya, wurin da aka ba ɗansa Finehas a ƙasar kan tudu ta Efraim.

  14. Haka Efraim ma bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka ci gaba da zama tare da su.

  15. Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.

  16. Da ya iso can, sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuma suka gangaro tare da shi daga tuddai, shi kuwa yana jagorarsu.

  17. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.

  18. Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne; Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka. Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro, daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito.

  19. Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara.

  20. To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.

  21. Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?

  22. Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim.

  23. Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske.

  24. Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”

  25. Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”