Skip to content

Assyria

115 verses · 5 known names

An kuma san shi da: Asshur, Assur, Assyrian, Assyrians

36.3500, 43.1500 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Assyria

Tace bisa littafi
  1. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala

  2. Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu.

  3. Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin.

  4. Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.

  5. A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.

  6. Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.”

  7. Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta.

  8. Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin.

  9. Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden.

  10. Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya.

  11. Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji.

  12. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.

  13. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku.

  14. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.

  15. har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can.

  16. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.

  17. Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.”

  18. Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.”

  19. Ubangiji kuma ya kasance tare da shi, ya yi nasara a duk abin da ya sa hannu. Ya yi tawaye ga sarkin Assuriya, ya ƙi yă bauta masa.

  20. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.

  21. Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.

  22. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.

  23. Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda.

  24. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.

  25. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.