Skip to content

Rabshakeh

16 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Rabshakeh

  1. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.

  2. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?

  3. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”

  4. Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”

  5. Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!

  6. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.

  7. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”

  8. Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.

  9. Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki,

  10. Sai sarkin yaƙin ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya. “ ‘Ga abin da babban sarki, sarkin Assuriya, ya faɗa. A kan me kake dangana wannan ƙarfin halinka?

  11. Sai Eliyakim, Shebna da Yowa suka ce wa sarkin yaƙin, “Ka yi haƙuri ka yi wa bayinka magana da Arameyanci, da yake muna jinsa. Kada ka yi mana magana da Yahudanci a kunnen mutanen da suke kan katanga.”

  12. Amma sarkin yaƙin ya amsa ya ce, “Kuna tsammani ga maigidanku da ku ne kawai maigidana ya aiko ni in yi waɗannan maganganu, ba ga mutanen da suke zama a kan katanga ba, waɗanda kamar ku, za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu?”

  13. Sa’an nan sarkin yaƙin ya tsaya ya kuma yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji kalmomin babban sarki, sarkin Assuriya!

  14. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da kuma Yowa ɗan Asaf marubuci suka tafi wurin Hezekiya, da rigunansu a kyakkece, suka kuwa faɗa masa abin da sarkin yaƙin ya yi ta farfaɗa.

  15. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”

  16. Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.