Skip to content

Isaiah

53 ayoyi · 3 'yan gida

An kuma san shi da: Esaias

Ayoyin da suka ambaci Isaiah

Tace bisa littafi
  1. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.

  2. Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya,

  3. Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su.

  4. Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya.

  5. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”

  6. Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa,

  7. Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.

  8. Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?”

  9. Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?”

  10. Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.

  11. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”

  12. Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji.

  13. Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”

  14. Sauran ayyukan mulkin Uzziya daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce ta hannun annabi Ishaya ɗan Amoz.

  15. Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan.

  16. Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.

  17. Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.

  18. Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.

  19. Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.

  20. Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.

  21. a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

  22. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,

  23. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.

  24. Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,

  25. sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo.