Skip to content

Gomorrah

23 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Gomorrha

31.1500, 35.4700 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Gomorrah

  1. har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.

  2. Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  3. suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar).

  4. Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim

  5. Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai.

  6. Sarakunan nan huɗu suka washe dukan kayayyakin Sodom da Gomorra, da kuma dukan abincinsu, sa’an nan suka tafi.

  7. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,

  8. Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama.

  9. Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.

  10. Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa.

  11. Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma. ’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.

  12. Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra.

  13. Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!

  14. Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.

  15. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  16. Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  17. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  18. “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  19. Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”

  20. Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.

  21. Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”

  22. in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah;

  23. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.