Tsallake zuwa abun ciki

Lot

34 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Lot

Tace bisa littafi
  1. Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.

  2. Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.

  3. Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran.

  4. Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.

  5. Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot.

  6. Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna.

  7. Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne.

  8. Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne.

  9. Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  10. Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna.

  11. Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom.

  12. Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma.

  13. Suka kuma kama Lot ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Sodom, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.

  14. Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane.

  15. Mala’ikun nan biyu suka iso Sodom da yamma. Lot kuwa yana zama a hanyar shiga birnin. Da ya gan su, sai ya tashi don yă tarye su, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  16. Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.”

  17. Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen

  18. Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar.

  19. Amma mutanen da suke ciki suka miƙa hannunsu, suka ja Lot zuwa cikin gida, suka rufe ƙofar.

  20. Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko ’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan,

  21. Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure ’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi.

  22. Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”

  23. Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri!

  24. A lokacin da Lot ya isa Zowar, rana ta hau.

  25. Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna.