Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ethiopia

48 ayoyi · 15 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha.

  2. Asa ya fita don yă ƙara da shi, suka ja dāgā yaƙi a Kwarin Zefata kusa da Maresha.

  3. Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”

  4. Ubangiji fa ya bugi mutanen Kush a gaban Asa da Yahuda. Mutanen Kush suka gudu,

  5. Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.

  6. Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can.

  7. Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima.

  8. Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush,

  9. wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku ’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba.

  10. Ku dukan mutanen duniya, ku da kuke zama a duniya, sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu, za ku gan shi, sa’ad da kuma aka busa ƙaho, za ku ji shi.

  11. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.”

  12. Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.

  13. Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci da kuma namun jeji; tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu, namun jeji kuma za su yi damina a kansu.

  14. a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

  15. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,

  16. haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.

  17. Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.

  18. A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”

  19. Amma Ebed-Melek mutumin Kush, wani hafsa a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin,

  20. Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa,

  21. “Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.”

  22. Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.”

  23. Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar.

  24. Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka,

  25. suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara.