Skip to content

Babylon

255 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Babylon's, Sheshach

32.5300, 44.4200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Babylon

Tace bisa littafi
  1. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.

  2. Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima;

  3. A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.

  4. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”

  5. Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji.

  6. Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”

  7. A zamani Yehohiyakim, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasar farmaki, Yehohiyakim dai ya zama abokin tarayyarsa na tsawon shekara uku. Daga baya kuma sai ya canja ra’ayi ya yi wa Nebukadnezzar tawaye.

  8. Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.

  9. A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.

  10. Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.

  11. Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku.

  12. Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.

  13. Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.

  14. Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.

  15. Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.

  16. A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.

  17. Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

  18. Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon.

  19. A rana ta bakwai na watan biyar, wadda ta zama shekara ta goma sha tara ta mulkin Sarki Nebukadnezzar na Babilon, Nebuzaradan, babban hafsan matsaran sarki, kuma bafadan sarkin Babilon, ya zo Urushalima

  20. Nebuzaradan babban hafsan matsaran, ya kwashi waɗanda suka rage a cikin birnin, tare da sauran jama’a, da waɗanda suka miƙa kansu ga sarkin Babilon, ya kai su bauta.

  21. Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.

  22. Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla.

  23. A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta.

  24. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zaɓi Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan yă zama shugaban sauran mutanen da suka rage a Yahuda.

  25. Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu.