Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jehoiachin

31 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yehohiyakim ya huta da kakanninsa. Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi.

  2. Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.

  3. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima.

  4. A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.

  5. Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.

  6. Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku.

  7. Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji.

  8. Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.

  9. Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.

  10. Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.

  11. A shekara ta talatin da bakwai ta bautar Yehohiyacin sarkin Yahuda, a shekaran da Ewil-Merodak ya ci sarautan Babilon, sai ya saki Yehohiyacin daga jaru, ya sake shi a rana ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu.

  12. Ya yi wa Yehohiyacin maganar alheri, ya kuma ɗaukaka shi sama da sauran sarakunan da suke tare da shi a Babilon.

  13. Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa.

  14. Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.

  15. Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,

  16. Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.

  17. Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  18. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.

  19. “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.

  20. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.

  21. Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.

  22. Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”

  23. Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?

  24. Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji!

  25. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”