Tsallake zuwa abun ciki

Nebuzaradan

15 ayoyi

An kuma san shi da: Nebuzar-adan

Ayoyin da suka ambaci Nebuzaradan

  1. A rana ta bakwai na watan biyar, wadda ta zama shekara ta goma sha tara ta mulkin Sarki Nebukadnezzar na Babilon, Nebuzaradan, babban hafsan matsaran sarki, kuma bafadan sarkin Babilon, ya zo Urushalima

  2. Nebuzaradan babban hafsan matsaran, ya kwashi waɗanda suka rage a cikin birnin, tare da sauran jama’a, da waɗanda suka miƙa kansu ga sarkin Babilon, ya kai su bauta.

  3. Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla.

  4. Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen.

  5. Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye.

  6. To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa,

  7. Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon

  8. Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.

  9. Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.

  10. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.

  11. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.

  12. Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.

  13. Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

  14. Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla,

  15. a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745. Jimillarsu duka 4,600 ne.