Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hamath

6 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer,

  2. sai ya aiki ɗansa Yoram wurin Sarki Dawuda yă gaishe, yă kuma yi masa barka saboda nasarar da ya yi a kan Hadadezer, gama Hadadezer nan ya hana Towu sakewa. Yoram ya tafi ɗauke da kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

  3. Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla.

  4. A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta.

  5. Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya,

  6. sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.