Skip to content

Ramah

17 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Ramath

31.8900, 35.2000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Ramah

  1. Akwai kuma Gibeyon, Rama, Beyerot,

  2. da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.

  3. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.

  4. Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.”

  5. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.

  6. Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.

  7. Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.

  8. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda.

  9. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.

  10. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.

  11. na Rama da Geba 621

  12. na Rama da na Geba 621

  13. da Hazor, da Rama, da Gittayim,

  14. Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce, “Za mu kwana a Geba.” Rama ta firgita; Gibeya ta Shawulu ta gudu.

  15. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.”

  16. Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.

  17. “Amon kakaki a Gibeya, ƙaho a Rama. Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen; ku ja gaba, ya Benyamin.