Skip to content

Baasha

26 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Baasha

Tace bisa littafi
  1. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.

  2. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.

  3. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”

  4. Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.

  5. Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.

  6. Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.

  7. Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki.

  8. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.

  9. A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu.

  10. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Yehu ɗan Hanani game da Ba’asha,

  11. Saboda haka ina gab da cinye Ba’asha da gidansa, zan kuma mai da gidanka kamar na Yerobowam ɗan Nebat.

  12. Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”

  13. Game da sauran ayyukan mulkin Ba’asha, abin da ya yi, da kuma nasarorinsa, an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  14. Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  15. Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.

  16. A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.

  17. Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki.

  18. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.

  19. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

  20. Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’

  21. Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya.

  22. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda.

  23. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”

  24. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.

  25. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.