Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Elah

9 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  2. Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.

  3. A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.

  4. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.

  5. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  6. Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki.

  7. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.

  8. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

  9. Game da sauran ayyukan mulkin Ela, da dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.