Tsallake zuwa abun ciki

Tirzah

13 verses

32.2700, 35.2900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Tirzah

  1. sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.

  2. Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu.

  3. Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.

  4. A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu.

  5. Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  6. A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.

  7. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.

  8. A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa.

  9. Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto.

  10. A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza.

  11. Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.

  12. A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu.

  13. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.