Tsallake zuwa abun ciki

Zimri

8 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Zimri

  1. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.

  2. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  3. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.

  4. A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa.

  5. Sa’ad da Isra’ilawa a cikin sansani suka ji cewa Zimri ya yi maƙarƙashiya a kan sarki, ya kuma kashe shi, sai suka yi shela, suka naɗa Omri, shugaban mayaƙa ya zama sarki a bisa Isra’ila, a wannan rana a cikin sansani.

  6. Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.

  7. Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  8. Yayinda Yehu ya shiga ƙofa, sai ta ce, “Lafiya, kai Zimri, mai kashe maigidansa?”