Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murder

131 ayoyi · 88 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.

  2. Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.

  3. Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka.

  4. In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”

  5. Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina.

  6. Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”

  7. Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.

  8. Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.

  9. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.

  10. “Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.

  11. Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”

  12. Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.

  13. Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”

  14. Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.

  15. Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.”

  16. Ba za ka yi kisankai ba.

  17. “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi.

  18. Amma in mutumin ya yi dabara har ya kashe wani mutum da gangan, sai a ɗauke shi daga bagadena a kashe shi.

  19. amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon. “Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata.

  20. “ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.

  21. Ko kuwa in wani yana riƙe da dutsen da ya isa yă kashe mutum a hannunsa, ya kuma harbi wani da dutsen har ya mutu, to, shi mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.

  22. Ko kuwa wani yana da makami na itace a hannunsa da ya isa yă kashe mutum, ya kuma bugi wani da shi har ya mutu, shi ma mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.

  23. Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.

  24. In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,

  25. ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.