Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murder

131 ayoyi · 88 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya.

  2. “ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.

  3. “ ‘Kada a karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don yă koma yă zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.

  4. “ ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.

  5. Kada ka yi kisankai.

  6. Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane,

  7. dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi.

  8. Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.

  9. Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.

  10. In aka sami an kashe mutum kwance a fili, a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, ba a kuma san wanda ya kashe shi ba,

  11. sai dattawanku da alƙalanku su je su gwada nisan wurin da gawar take zuwa garuruwan da suke maƙwabtaka.

  12. Sai dattawan garin da suke kurkusa da gawar su ɗauki karsanar da ba a taɓa yin aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba,

  13. a gangara da ita kwarin da ba a taɓa nome, ko shuki a ciki ba, inda kuma akwai rafi mai gudu, a can cikin kwarin za su karye wuyanta.

  14. Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci.

  15. Sa’an nan dukan dattawan garin da yake kurkusa da gawar za su wanke hannuwansu a bisa karsanan da aka karye wuyar a kwarin,

  16. za su kuma furta, “Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga an yi haka ba.

  17. Karɓi wannan kafara saboda mutanenka Isra’ila, wanda ka fansar, ya Ubangiji, kada kuma ka ɗaura wa mutanenka alhakin jinin mutumin nan marar laifi.” Za a kuwa yi kafarar zub da jinin da aka yi.

  18. Ta haka za ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga cikinku, da yake kun yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

  19. Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa, gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa; zai ɗau fansa a kan abokan gābansa yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa.

  20. Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya.

  21. Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa.

  22. Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ”

  23. To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.

  24. Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.

  25. Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba.