Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murder

131 ayoyi · 88 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa.

  2. Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.

  3. Sai sarki ya umarci Benahiya ya ce, “Yi kamar yadda ya faɗa. Ka kashe shi, ka kuma binne shi, ka wanke ni da gidan mahaifina daga laifin jini marasa laifin da Yowab ya zubar.

  4. Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi.

  5. Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.

  6. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  7. Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake.

  8. Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane.

  9. Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.”

  10. Sa’an nan ’yan iska biyu suka zo, suka zauna ɗaura da shi, suka kawo zarge a kan Nabot a gaban mutane, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” Saboda haka aka ɗauke shi waje da birnin, aka jajjefe shi da dutse har ya mutu.

  11. Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ”

  12. Sa’an nan ya ɗauki ɗansa na fari, wanda zai gāje shi, ya yi hadaya da shi a bisa katangan birnin. Isra’ilawa suka firgita ƙwarai; sai suka janye suka koma ƙasarsu.

  13. Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”

  14. Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.

  15. Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel.

  16. Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’ ”

  17. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.

  18. Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

  19. Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”

  20. Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.

  21. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.

  22. Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka; daga kwanton yakan kashe marar laifi. Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye.

  23. Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa.

  24. Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa.

  25. Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.