Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murder: Rechab

3 ayoyi · 88 fannoni

Ayoyi game da Rechab

  1. To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.

  2. Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.

  3. Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba.